Yawan kudin da Sin ta kebe wajen yin nazari da raya sana'o'i ya kai kashi 2 cikin 100 na GDP na kasar
Bisa labarin da wakilinmu ya samu daga taron kimiyya da fasaha na kasar Sin da aka shirya kwanan baya a nan birnin Beijing, an ce, yawan kudin da Sin ta kebe wajen yin nazari, da gwajin aiki don raya zamantakewar al'umma, ya kai kudin Sin RMB sama da biliyan dubu 1, kuma abin da ya kai kashi 2 cikin 100 na yawan kudin da aka samu wajen samar da kayayyaki wato GDP na kasar, cikinsu yawan kudin da masana'antu suka yi amfani da su wajen nazari da habakar sana'o'insu ya kai kashi 74 cikin 100.
Ministan kimiyya da fasaha na kasar Sin Wan Gang, ya bayyana cewa, a cikin shekaru 5 da suka gabata, harkokin kimiyya da fasaha na Sin sun habaka cikin gaggawa, kuma Sin ta kara daukaka matsayinta wajen kirkiro sabbin abubuwa, kuma yawan ci gaba da aka samu sakamakon raya harkokin kimiyya da fasaha ya karu, haka nan matsakaicin yawan kudin da kasar ta zuba wajen yin nazari ya kan karu a ko wace shekara da kashi 23 cikin 100, da haka Sin ta zama kasa mai samun babban ci gaba a fagen krikiro sabbin abubuwa.(Bako)