in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Karuwar GDP na kasar Sin a shekara 2013 zai haura kashi 8 cikin 100, inji wani kwararre
2012-12-30 16:16:13 cri

Wani kwararre ya yi hasashen cewa, karuwar alkaluman GDP na kasar Sin a shekara mai zuwa, za ta haura kashi 8 cikin 100, sannan ya yi hasashen karuwar farashin kayayyaki fiye da na wannan shekara.

Lu Zhongyuan, mataimakin darektan cibiyar bunkasa bincike wadda ke karkashin hukumar gudanarwar Sin, ya ce babu wata tantama tattalin arzikin kasar Sin, zai karu da sama da kashi 8 cikin 100 a shekara ta 2013, sannan kamata ya yi gwamnati ta kara mayar da hankali kan inganta ci gaba mai dorewa tare da jure matsalar da hauhawar farashin kayayyakin daga ketara za ta haifar.

Lu ya ce, tun watan Yunin wannan shekara ne, tattalin arzikin kasar Sin ya sauka kasa, sakamakon matakan gyare-gyaren tattalin arzikin kasar, tsare-tsaren barin kasuwa ta yi halinta, ya kara da cewa, wadannan abubuwa su ne za su ci gaba da ingiza ci gaban tattalin arzikin a wannan shekara.

A ranar 18 ga watan Janairun shekara ta 2013 ne, aka shirya hukumar kididdiga ta kasar Sin, za ta bayyana ci gaban GDP na kasar na watanni 3 na karshe na shekara ta 2012 da kuma na baki dayan shekarar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China