Rahoton ya yi kiyasin cewa, a kokarin cimma wannan buri, dole ne saurin karuwar GDP ya kai kashi 7.1 cikin dari a kowace shekara. A shekaru 10 masu zuwa kuma, saurin karuwar GDP zai kai kashi 7.5 zuwa 8 cikin dari a kowace shekara.
Ban da haka, rahoton ya ce, a shekarar 2012, a kuma lokacin da ake fuskantar matsalar basusukan kasashen Turai da raguwar bunkasuwar tattalin arzikin duniya, Sin ta gamu da matsaloli da yawa wajen bunkasa tattalin arziki. Amma bisa karuwar bukatun cikin gida, yawan jarin da aka zuba ya karu cikin sauri. Dadin dadawa, a sakamakon rashin samun farfadowar tattalin arziki ta kasashe masu sukuni, bukatu daga ketare sun ragu sosai. Duk da haka dai, ana cikin yanayi mai kyau na neman samun guraben aikin yi, yawan kudin shiga na jama'ar kasar Sin na karuwa cikin sauri, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ya ragu. Wannan ya yi nuni da cewa, kawo yanzu ana cikin hali mai kyau a fannin tattalin arziki a kasar.(Fatima)