Bankin duniya ya tabbatar da cewa, yawan karuwar GDP na kasar Sin ba zai kai kashi 8 cikin dari ba, sabo da raguwar hajojin da kasar Sin ta fitar zuwa kasashen waje, da kuma ragin kudaden da ke gudana a kasuwannin zuba jari. Amma bisa hasashen da aka yi, yawan karuwar GDP na Sin zai karu zuwa kashi 8.1 cikin dari a shekarar 2013, sakamakon wasu matakan da ta dauka na bunkasa tattalin arziki da kuma goyon baya da take samu dangane da karuwar cinikayya a dukkanin fadin duniya.
Shugaban bankin duniya Jim Yong Kim, ya nuna cewa, a cikin shekaru 20 da suka gabata, karfin tattalin arzikin yankunan gabashin Asiya da tekun Pacific ya ribanya har da ninki biyu daga cikin tattalin arziki na duk fadin duniya, wato daga kashi 6 cikin dari zuwa kashi 18 cikin dari na yanzu, halin zai taimaka matuka ga habakar tattalin arzikin ragowar kasashen. (Maryam)