Habakar a wannan zango ta kasance mafi koma baya a zanguna goma. A farkon shekara ta 2011, Sin ta kafa muradin cimma kashi 8 ne a baki dayan shekarar, bayan da tattalin arzikinta ya habaka zuwa kashi 10.3 a shekara ta 2010.
A yayin wani taron manema labarai, Ma Jiantang, shugaban cibiyar NBS ya ce, tattalin arzikin kasar ya dadu da kashi 2 a zango na hudu, bisa la'akari da tafiyar tattalin arzikin ta zango-zango.
Wata kididdigar farko ta nuna cewa, GDP na kasar ya kai yuan tiriliyan 47.16, kwatankwacin dalar Amurka tiriliyan 7.26 a shekara ta 2011, in ji Ma Jiantang.
Ya kuma bayyana cewa, yadda tattalin arzikin kasar ya tafi a shekara ta 2011, wani kyakkyawan mafari ne, ga tsarin gudanar da harkoki cikin shekaru biyaar na kasar a karo na goma sha biyu wato daga shekara ta 2011 zuwa ta 2015, kana hakan ya tafi daidai da dokar tafiyar da tattalin arziki mafi girma. (Garba)