Hukumar kididdigar ta kasar Sin ta kira wani taron manema labaru a ranar Jumma'a 18 ga wata a ofishin yada labaru na majalisar gudanarwa, inda ta bayyana yadda Sin ta raya tattalin arzikinta a shekarar 2012.
Shugaban hukumar Ma Jiantang ya bayyana cewa, jimillar GDP na shekarar 2012 ya kai kudin Sin Yuan biliyan 51,932.2, wanda ya karu da kashi 7.8 bisa dari idan an kwatanta da bara waccan.
Ban da haka, yawan kudin da Sinawa suka kashe wajen sayayya ya karu da kashi 2.6 cikin dari bisa na shekarar 2011. Daga cikinsu, a cikin birane an samu karuwar kashi 2.7 bisa dari, yayin da a kauyuka an samu karuwar kashi 2.5 bisa dari .
Ma Jiantang ya nuna cewa, Sin za ta ci gaba da yin tsayin daka kan raya tattalin arziki bisa hanyar da ta dace, da kuma kara kwaskwarimar da take yi wajen sauyin hanyar samun bunkasuwa.
Mr. Ma ya ce, ya kamata, a mai da muhimmanci sosai wajen samun bunkasuwar tattalin arziki da moriya cikin karko tare da kara bude kofa ga kasashen waje, sannan a kara ingiza matakan da gwamnatin za ta dauka dangane da tattalin arziki, har ma da ba da tabbaci ga zaman rayuwar jama'a da samun bunkasuwar tattalin arziki da raya al'umma cikin jituwa kuma cikin dogon lokaci. (Amina)