Kakakin hukumar kididdiga ta kasar Sin Sheng Laiyun ya nuna a yau ranar 15 ga wata a nan birnin Beijing cewa, jimlar GDP ta kasar Sin a cikin farkon watanni uku na shekarar bana ta kai kudin Sin Yuan biliyan 11885.5 wanda ya karu da kashi 7.7 cikin dari bisa na makamancin lokacin bara.
A ganinsa, a cikin watanni uku da suka gabata, Sin ta nace kan manufar samun bunkasuwa mai karko, kuma za ta mai da muhimanci don kara samun inganci da moriya a fannin bunkasa tattalin arziki, da kyautata manufar yin kwaskwarima da sa ido kan manyan sauye-sauye, tare kuma da kawo wasu sabbin gyare gyare kan ayyukan gwamnati, sannan da karkata hanyar samun bunkasuwar tattalin arziki ta yadda za a samu bunkasuwar tattalin arzikin kasa cikin daidaici.
Sheng Laiyun ya ce, abin da ya fi muhimmanci da za a yi nan gaba shi ne samun bunkasuwa mai karko da sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin kasar yadda ya kamata, da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a. (Amina)