Kididdigar da aka bayar a karshe ta nuna cewa, yawan karuwar da aka samu daga sha'anin noma ya kai kashi 10.1 cikin 100 bisa na dukkan jimillar da aka yi , a yayin da bangaren masana'antu ya kai kashi 46.7 bisa 100, a sha'anin aikin hidimomi na yau da kullin kuma, addadin ya kai kashi 43.2 bisa 100.
Hukumar ta samu fasaha mai kyau, ta hanyar yin koyi da kasashen duniya domin gabatar da hakikanin halin bunkasuwar tattalin arzikin al'ummar kasar Sin. Tun daga shekarar 2003, ta yi wa tsarin kididdiga kwaskwarima har sau biyu. Sabon tsarin ya kunshe muhimman matakai guda biyu, da su hada da yin kididdiga a zagaye na farko da na karshe, abun da zai inganta kididdigar da aka gabatar sau biyu.(Amina)