Firaministan kasar Sin Wen Jiabao ya furta a gun taro karo na 5 na majalisar wakilan jama'ar kasar na 11 da aka bude a ran 5 ga wata cewa, an kafa burin yawan karuwar GDP na wannan shekara na kasar wanda zai kai kashi 7.5 cikin dari, kuma yawan hauhawar farashin kayayyaki (CPI) ba zai wuce kashi 4 cikin dari ba.
Wen Jiabao ya jaddada a yayin da ya bayar da rahoton ayyukan gwamnati a gun taron cewa, an rage burin yawan karuwar GDP ne domin ya dace da shirin shekaru biyar biyar na 12, wato gaggauta gyara hanyar bunkasuwar tattalin arziki da kara ingancin bunkasuwar tattalin arziki domin neman samun bunkasuwa mai dorewa da kuma inganci. Ban da haka kuma, kasar za ta amince da yawan karuwar CPI da zai kai kashi 4 cikin dari sabo da la'akari da tasirin da tattalin arzikin kasashen waje zai kawo wa kasar Sin da kuma yanayin zaman rayuwar jama'a, ta yadda kuma za a iya yin gyare-gyare kan farashin kayayyaki bisa abin da aka kayyade.
Bugu da kari, Wen Jiabao ya bayyana cewa, za a yi kokarin cimma burin samar da sabbin guraban ayyukan yi har miliyan 9 ko fiye a birane da garuruwa, kuma yawan mutanen da suka rasa guraban ayyukan yi ba zai wuce kashi 4.6 cikin dari ba, sannan yawan karuwar kayayyakin shigi da fici zai kai kashi 10 cikin dari, domin ci gaba da kyautata yanayin kudin shigi da fici.(Lami)