Yang Jiechi ya cimma nasara a wajen ziyarar da ya kai wa kasar Morocco Mr. Yang Jiechi ya ziyarci kasar Morocco ne daga ran 11 zuwa ran 12 ga wata. Wannan ne karo na farko da ya ziyarci kasar Morocco bayan da ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin a shekarar 2007. Jakadar kasar Sin dake Morocco Xu Jinghu tana ganin cewa, ziyarar da Yang Jiechi ya yi ta samar da sakamako mai kyau, kuma ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Morocco a dukkan fannoni.