in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ganawa tsakanin firaministan kasar Morocco da ministan harkokin waje na Sin Yang Jiechi
2010-01-13 09:07:30 cri

A ran 12 ga wata, a Rabat, babban birnin kasar Morocco, firaministan kasar Morocco Abbas el Fassi ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi dake yin ziyara a kasar.

Malam Fassi ya bayyana cewa, kasar Morocco ta darajanta dangantakar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakaninta da Sin, kuma tana son kara hadin gwiwa da kasar Sin daga dukkan fannoni, da yin kokarin ingiza bunkasuwar dangantakar dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Morocco ta nuna babban yabo ga kasar Sin da ta dauki sabbin matakai don hada kai da kasashen Afrika, kuma tana fatan za a kara hadin giwwa a tsakanin kasashen biyu bisa tsarin hadin kai a tsakanin Sin da Afrika, da sa kaimi kan bunkasuwar dangantakar dake tsakanin Sin da Afrika.

Malam Yang Jiechi ya furta cewa, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Morocco don kara yin mu'amala da hadin gwiwa a kan batutuwan kasashen duniya da na yankuna, ta yadda za a ci gaba da bunkasa dangantakar abokantaka dake tsakanin kasashen biyu.

Malam Yang Jiechi ya kara da cewa, gwamnatin Sin ta dora muhimmanci kan tabbatar da ayyuka bayan taron ministoci a karo na hudu na dandalin tattaunawar hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afrika, kuma tana son kara yin mu'amala da hada kai da kasar Morocco da sauran mambobin dandalin tattaunawar don gudanar da ayyuka daban daban da kyau.(Asabe)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China