in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da wakilai na CRI da gidan rediyo na kasar Kenya
2010-01-08 21:23:17 cri

Tun daga ranar 6 zuwa 8 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya kai ziyara a kasar Kenya. Yayin da yake ziyara, ya bayyana wa 'yan jaridan gidan rediyo na kasar Sin wato CRI da gidan rediyo na kasar Kenya cewa, ya kai ziyara a kasashen Afirka ne da nufin zurfafa dangantakar abokantaka bisa manyan tsare-tsare a tsakanin Sin da kasashen Afirka.

Kasar Kenya ita ce ta farko da Yang Jiechi ya kai ziyara a sabuwar shekara, bayan haka zai kai ziyara a kasashen Nijeriya da Saliyoda Algeria da Morocco da kuma Saudiyya. Yang Jiechi ya yi imani cewa, dangantaka tsakanin Sin da kasashen Afirka suna samu ci gaba. A fannin siyasa, shugabannin bangarorin biyu sun kiyaye yin mu'amala da juna don kara amincewa juna kan tsare-tsaren Sin da kasashen Afirka. A fannin tattalin arziki, an inganta dangantakar cinikayya tsakanin Sin da kasashen Afirka, kana an kara zuba jari tsakaninsu. A fannin al'adu, suna yin mu'amala tsakaninsu.(Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China