in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi ganawa tsakanin shugaban kasar Kenya da Mr Yang Jiechi
2010-01-07 09:24:46 cri

A ranar 6 ga wata a Nairobi babban birnin kasar Kenya, shugaban kasar Kenya Mwai Kibaki ya gana da ministan harkokin waje na Sin Yang Jiechi wanda yake ziyara a can.

Kibaki ya ce, a matsayin abokiyar mafi girma gare Kenya, kasar Sin ta yi hadin kai tare da Kenya domin taimaka mata wajen gina manyan ayyukan more rayuwar jama'a, kuma ta taka mihimmiyar rawa wajen ba da taimako ga Kenya ta fuskar gina hanyoyin mota da dai sauransu ayyuka, hakan ya sa ba ma kawai taimakon da Sin ta bayar ya amfanawa jama'ar Kenya ba, hatta ma ya amfanawa bunkasuwar yankin Afrika ta gabas, saboda haka, gwamnatin Kenya da jama'arta sun nuna yabo sosai ga kasar Sin. Ban da wannan kuma, Kenya tana tsayawa tsayin daka kan manufar kasar Sin daya tak, kuma tana fatan hada kai da kasar Sin domin kara sa kaimi ga bunkasuwar dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci dake tsakanin kasashen biyu.



Yang Jiechi kuma ya fadi cewa, bangaren Sin tana dora babban muhimmanci kan dangantakar dake tsakanin kasashen biyu, kuma tana fatan yin kokari tare da Kenya domin kara yin musaya tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kara yin mu'amala tsakanin jama'arsu, da kara hada kai ta fuskar gina manyan ayyukan more rayuwar jama'a da sauran fanonni ta yadda za a kara ciyar da dangantakar dake tsakanin kasashen biyu gaba.(Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China