in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya za ta kara samun ingantuwa a sabuwar shekara
2010-01-09 16:59:08 cri
Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya fara ziyararsa a kasar Nijeriya a ran 8 ga wata bisa gayyatar da takwaransa na kasar Nijeriya Ojo Maduekwe ya yi masa.

Yayin da Yang Jiechi ke yin shawarwari tare da Mr. Maduekwe, ya waiwayi dangantakar da ke tsakanin Sin da Nijeriya. Kuma ya bayyana cewa,

"Kasashen Sin da Nijeriya sun tabbatar da kulla huldar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare tun a shekara ta 2005. Bayan wancan lokaci kuma, an ci gaba da raya dangantakar yadda ya kamata. Bisa abubuwan da aka tanada a cikin dangantakar, ba kawai ya kamata a nuna amincewar juna a fannin siyasa ba, hatta ma kamata ya yi a yi haka ne a fannonin tattalin arziki da al'adu."

Gaskiya ne, ana raya dangantakar abokantaka a tsakanin Sin da Nijeriya bisa manyan tsare-tsare daga dukkan fannoni. A yayin babban taron sauyawar yanayi ta Copenhagen, Sin da Nijeriya abokan kawance ne, kuma Sin ta nuna goyon baya ga bukatun da kasashen Afirka suke da su. A fannin cudanyar tattalin arziki da cinikayya, ko da yake matsalar kudi ta duniya ta kawo illa sosai gare su, amma jimillar cinikayyya a tsakanin kasashen biyu a shekara ta 2009 ta kai dala biliyan 6.5, yayin da yawan kudin kayayyakin da Nijeriya ta fitar da su zuwa kasar Sin ya karu da kusan kashi 50 cikin kashi dari. A fannin al'adu kuma, yawan daliban kasar Nijeriya da suka zo Sin don kara ilmi yana ta karuwa a ko wace shekara, haka kuma an kafa kwalejin Confucius a jami'o'i biyu na kasar Nijeriya don yada al'adun gargajiya na Sin. Mr. Maduekwe, ministan harkokin waje na kasar Nijeriya ya furta cewa, yanzu dangankatar da ke tsakanin kasashen biyu tana cikin zamani mafi kyau a tarihi. Kuma ya ce,

"takwarata na kasar Sin wato Yang Jiechi ya kawo ziyara a Nijeriya ne ba kawai domin karfafa ra'ayi bai daya da shugaba Umaru Yar'Adua na Nijeriya da shugaba Hu Jintao na Sin suka samu yayin da shugaba Yar'Adua ya kai ziyara a Sin a shekara ta 2008 ba, hatta ma ya yi ziyarar ne domin inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu. Tabbas ne za a kara ciyar da dangankar zuwa gaba bayan ziyarar."

Mr. Yang Jiechi ya nuna amincewa da wannan, kuma ya ce,

"kasar Nijeriya wata muhimmiyar kasa ce a Afirka har ma a duk duniya, wadda ke bayar da babbar gudummowa a fannonin kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali kana da samun bunkasuwar shiyya-shiyya da duniya, don haka Sin ta nuna mata yabo sosai. A nan gaba, za mu inganta hadin gwiwa tare da Nijeriya domin kara sa kaimi ga samun zaman lafiya da bunkasuwar duniya gaba daya."(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China