in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya cimma nasara a wajen ziyarar da ya kai wa kasar Morocco
2010-01-14 14:55:31 cri

Jakadar kasar Sin dake kasar Morocco Xu Jinghu ta bayyana a ran 12 ga wata cewa, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya cimma nasarar yin ziyara a kasar Morocco.

Mr. Yang Jiechi ya ziyarci kasar Morocco ne daga ran 11 zuwa ran 12 ga wata. Wannan ne karo na farko da ya ziyarci kasar Morocco bayan da ya zama ministan harkokin waje na kasar Sin a shekarar 2007. Jakadar kasar Sin dake Morocco Xu Jinghu tana ganin cewa, ziyarar da Yang Jiechi ya yi ta samar da sakamako mai kyau, kuma ta karfafa hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Morocco a dukkan fannoni. Ta ce, "Wannan ziyara ta samar da sakamako da yawa. A yayin ziyararsa, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya gana da firaministan kasar Morocco Abbas El Fassi, kuma ya yi shawarwari tare da Taib Fassi Fihri ministan harkokin waje da hadin gwiwa na kasar Morocco, inda bangarorin biyu suka yi musayar ra'ayi kan huldar dake tsakaninsu da batutuwan duniya da suka fi janyo hankalinsu, sa'an nan kuma sun cimma matsaya daya a fannoni daban daban. Ban da haka kuma, ministocin harkokin waje na kasashen biyu sun kulla wata yarjejeniya don nuna amincewa da tsarin tattalin arziki iri na kasuwanci da kasar Sin take bi da kuma sa hannu kan wata takardar samar wa kasar Morocco kudin agaji wanda yawansa ya kai kudin Sin Yuan miliyan 1 da dubu 500. Amincewa da tsarin tattalin arziki iri na kasuwanci da kasar Sin take bi yana da babbar ma'ana ga bunkasa cinikayya a tsakanin kasashen biyu. Kuma ziyarar Yang Jiechi za ta kawo moriya ga bunkasuwar huldar abokantaka ta hadin gwiwa a tsakanin kasashen biyu a dukkan fannoni."

1 2 3
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China