in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Hadin gwiwar tattalin arziki dake tsakanin kasashen Sin da Nijeriya tana samun bunkasuwa cikin sauri
2010-01-09 20:10:51 cri

A ran 8 ga wata da dare, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya gana da wakilin gidan talibijin na kasar Nijeriya wato NTA, inda ya ce, a shekarun baya, hadin gwiwar dake tsakanin kasashen Sin da Nijeriya a fanonin tatalin arziki da ciniki tana samun bunkasuwa cikin sauri. Kasashen biyu sun taimakawa juna sosai, suna da kyakkyawar makomar yin hadin gwiwa.

Yang Jiechi ya ce, yawan kudin da kasashen suka samu wajen yin ciniki a tsakaninsu ya ninka sau 2 daga shekarar 2003 zuwa shekarar 2008, wanda ya kai dalar Amurka biliyan 7 da miliyan 266, yawan kudin da kamfanonin Sin suka zuba a kasar Nijeriya ya kai fiye da dalar Amurka biliyan 6 da miliyan 500. Kuma kasashen biyu sun yi hadin gwiwa a fannoni da yawa ciki har da makamashi da sadarwa da aikin gona da ayyukan sararin samaniya da manyan ayyukan yau da kullum da hada-hadar kudi da kuma sauransu. Kamfanonin Sin sun shiga sana'o'i da yawa na kasar Nijeriya, kana kamfanonin kasar Nijeriya suna kokarin neman damar yin ciniki a kasar Sin.

Yang Jiechi ya ce, kasar Sin tana son neman samun sabbin hanyoyi da ayyuka don yin hadin gwiwa da kasar Nijeriya, musamman ma ayyukan gona da kera kayayyaki da kimiyya da fasaha. Aikin kimiyya da fasaha muhimmin aiki ne da kasashen Sin da Nijeriya suka yi hadin gwiwa a kai, duk da cewar ana matakin farko wajen yin irin wannan hadin gwiwa, amma tana da kyakkyawar makoma a nan gaba.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China