in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi shawarwari tsakanin ministan harkokin waje na Sin da takwaransa na kasar Morocco
2010-01-12 09:20:00 cri

A ranar 11 ga wata a Rabat babban birnin kasar Morocco, ministan harkokin waje na Sin Mr Yang Jiechi wanda ya kai ziyara a kasar ya yi shawarwari tare da ministan kula da harkokin diplomasiyya da hadin kai na kasar Taib El Fassi Fihri.


Bangarorin biyu sun darajanta ci gaban da aka samu ta fuskar siyasa da cinikayya da kuma al'adu da kiwon lafiya da sauransu a cikin shekaru 52 da kafuwar dangankatar diplomasiyyar dake tsakaninsu, ban da wannan kuma, sun amince da kara yin mu'amala tsakanin shugabannin kasashen biyu, da kuma kara amincewa juna a fannin siyasa, da zurfafa hada kai, da kara musanyar ra'ayoyi, da kuma kara yin shawarwari da hada kai ta fuskar ayyukan kasa da kasa da yankuna, hakan ya sa dangantakar sada zumunci dake tsakanin kasashen biyu ta kara samun bunkasuwa.


Bayan shawarwarin da suka yi, ministocin harkoki waje na kasashen biyu sun sa hannu kan sanarwar amince da matsayin tattalin arziki na kasuwar kasar Sin (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China