in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Maldives Mohamed Nasheed ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi
2010-01-06 10:19:35 cri

A ranar 5 ga wata, a birnin Male hedkwatar kasar Maldives, shugaban kasar Mohamed Nasheed ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin Mr. Yang Jiechi wanda ke yin ziyarar aiki a kasar.

Yang Jiechi ya ce, kasar Sin tana fatan yin kokari tare da kasar Maldives a karkashin ka'idoji 5 na kasancewa tare cikin lumana, da girmamawar manyan batutuwan da ke shafar bangarorin biyu, da inganta dangantakar sada zumunci na gargajiya tsakaninsu, da karfafa hakikanin hadin gwiwa a fannonin tattalin arziki da cinikayya da yawon shakatawa da sana'ar kamun kifaye tsakaninsu, domin ingiza samun dauwamammen bunkasuwar dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci tsakaninsu. Yang Jiechi ya ce, kasar Sin tana fatan ci gaba da hadin gwiwa tare da kasar Maldives, domin warware batun sauyin yanayi, cikinsu har da kiyaye moriyar kasashe masu tasowa da kasashen da ke kananan tsibirai.

Nasheed ya ce, Maldives tana jinjinawa muhimmiyar rawar da kasar Sin ta taka a gun taron Copenhagen kan batun sauyin yanayi na duniya, yana fatan bangarorin biyu za su ci gaba da inganta hadin gwiwa tsakaninsu, domin warware batun sauyin yanayi na duniya da dai sauran manyan batutuwan duniya. Kasar Maldives tana fatan yin kokari tare da kasar Sin, da inganta hadin gwiwa ta fuskar yawon shakatawa da sana'ar kamun kifaye, domin ingiza samun bunkasuwar dangantakar hadin gwiwa ta sada zumunci tsakaninsu.(Bako)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China