in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mataimakin shugaban Nijeriya ya gana da ministan harkokin waje na kasar Sin
2010-01-09 15:09:11 cri

Mataimakin shugaban Nijeriya ya gana da Mr. Yang Jiechi

Ran 8 ga wata, a birnin Abuja, hedkwatar kasar Nijeriya, Goodluck Jonathan, mataimakin shugaban kasar Nijeriya ya gana da Yang Jiechi, ministan harkokin waje na kasar Sin, wanda ke yin ziyarar aiki a kasar.

A yayin ganawar, Mr. Yang ya bayyana cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da Nijeriya domin ci gaba da inganta fahimtar juna da amincewa da juna, da daukar hakikanin matakan sa kaimi kan yin hadin gwiwa a harkokin tattalin arziki da ciniki, da kara tuntubar juna da taimakawa juna a harkokin da suka shafi bangarori daban daban, da kuma rika kyautata huldarsu bisa manyan tsare-tsare.

Mr. Yang ya kuma kara da cewa, gwamnatin Sin na sa muhimmanci sosai kan karin ayyukan da aka tsara bayan taron ministoci a karo na 4 na dandalin tattaunawa kan yin hadin gwiwa a tsakanin Sin da Afirka, tana son inganta tuntubar juna da taimakawa juna a tsakaninta da Nijeriya da sauran kasashe mambobin dandalin wajen aiwatar da sabbin matakai 8 da Sin ta gabatar na yin hadin gwiwa da Afirka.

Mr. Yang Jiechi ya gana da takwaransa na kasar Nijeriya

A nasa bangaren kuma, Mr. Jonathan ya darajanta hulda a tsakanin Nijeriya da Sin. Ya kuma kara da cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa wajen samun sakamako a yayin taron Copenhagen. Ta ba da muhimmiyar gudummawa wajen inganta hadin gwiwa a tsakanin kasashe masu tasowa. Nijeriya ta nuna babban yabo kan wannan. Sa'an nan kuma, Nijeriya tana son hada kai da kasar Sin a fannonin kara inganta da raya hadin gwiwar abokantaka a tsakanin kasashen 2, da kuma bunkasa dangantakar abokantaka a tsakaninsu bisa manyan tsare-tsare zuwa sabon mataki. Haka zalika, Nijeriya ta sake nanata bin manufar "kasar Sin daya tak a duniya".(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China