in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya ziyarci kasashen Afrika
2010-01-05 21:10:27 cri

A ran 5 ga wata, ministan harkokin waje na kasar Sin Yang Jiechi ya kai ziyara a karo na farko a shekarar 2010 a kasashe 6 na Afrika da kuma kasar Maldives. Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Jiang Yu ta bayyana a ranar cewa, wannan ne karo na 20 da ministan harkokin waje na kasar Sin ya kai ziyarar farko a kasashen Afrika a cikin kowace sabuwar shekara.

Jiang Yu ta ce, Yang Jiechi zai ziyarci kasar Kenya daga ran 6 zuwa ran 7 ga wata, kuma zai kai ziyara a kasar Nijeriya daga ran 7 zuwa ran 9 ga wata, sannan kuma, zai ziyarci kasashen Saliyo da Algeria da Morocco daga ran 9 zuwa ran 12 ga wata, daga bisani kuma zai ziyarci kasar Saudiyya daga ran 12 zuwa ran 13 ga wata.

Gwamnatin Sin za ta yi kokari tare da kasashen Afrika wajen tabbatar da sakamakon da aka samu a gun taron ministoci na 4 don raya huldar abokantaka mai sabon salo a tsakanin Sin da kasashen Afrika bisa ka'idojin sada zumunci da nuna sahihanci da zaman daidaito da kawo moriyar juna da neman samun bunkasuwa tare, ta yadda jama'ar Sin da kasashen Afrika za su kara cin gajiyar kyakkyawan sakamakon da aka samu ta hanyar yin hadin gwiwa a tsakaninsu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China