A ran 5 ga wata, bankin tsakiya ta kasar Nijeriya ta ce, yawan GDP da kasar ta samu a shekarar 2009 ya karu da kashi 6.9%, wanda ya karu da 1% bisa na shekarar 2008, kana ya karu bisa zaton da bankin duniya ta yi kan karuwar tattalin arzikin yankin kudancin Sahara wato kasa da kashi 5%.
Shugaban bankin tsakiya na kasar Nijeriya Lamido Sanusi ya bayyana cewa, muhimmin dalilin da ya sa tattalin arzikin kasar ya samu bunkasuwa ba domin sana'ar man fetur kawai ba, saidai a ce aikin noma da sana'ar yawon shakatawa da sana'ar sadarwa suka taimaka kwarai wajen wannan bunkasa. Karuwar sana'ar kere-kere ba ta kai kashi 1% a cikin karuwar GDP ba, amma karuwar aikin noma ta kai fiye da 40% a cikin karuwar GDP.
Mr Sanusi ya ce, karuwar tattalin arziki ba ta samar da karin damar samun aikin yi ba, domin sana'ar kere-kere da ta fi samar da aikin yi tana fuskantar matsalolin ayyukan yau da kullum marasa ci gaba da rashin tallafin bayar rancen kudi.(Zainab)