logo

HAUSA

An tabbatar da bullowar cutar kwalara a yankin Zinder

2024-09-20 11:40:21 CMG Hausa

A yankin Zinder na jamhuriyyar Nijar, ta hanyar wata sanarwar ce, a ranar jiya Alhamis 19 ga watan Satumban shekarar 2024, ofishin ma’aikatar kiwon lafiya na yankin ya sanar da bullowar cutar amai da gudanawa ko kwalara, tare da janyo farga ba a cikin zukatan al’umma.

Daga birnin Yamai,abokin aikin mu Mamane Ada ya aiko mana da wannan rahoto.

Ofishin ma’aikatar kiwon lafiya dake cikin yankin Zinder ko Damagaram ya sanar da barkewar wannan cutar amai da gudanawa ko kwalara a cikin yankin, musamman ma cikin jihar Mirriah da kuma birnin Zinder tare da cewa, hukumomin kiwon lafiya na wuraren sun tabbatar da mutum 74 da aka tabbatar sun harbu da wannan cutar inda biyu daga cikinsu suka kwanta dama.

A cewar hukumomin kiwon lafiya na yankin, a yanzu haka ana ci gaba da daukar nauyin marar lafiya, tare da daukar matakan kariya, domin ganin an dakile yaduwar cutar zuwa sauran jihohin yankin Zinder dake kusa da ma wuraren da cutar ta bayyana.

Haka kuma ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa a cikin sanarwar ta bayyana daukar kwararrun matakai na ganin an dakile wannan cuta ta amai da gudanawa dake saurin yadawa ta hanyar iska da mu’amala.

Kowace shekara a lokaci makamancin haka, yankin Zinder na fama da cutar kwalara, ganin yadda aka samu ruwan sama sosai a wannan shekara tare da haddasa ambaliyar ruwa a yawancin yankunan kasar Nijar, ma’aikatar kiwon lafiya ta kasa tare da kungiyoyi masu zaman kansu na fargabar yadu sauran cutuka kamar zazzabin cizon sauro da cutar amai da gudanawa, inda har ba a dauki matakan da suka dace ba, musammun ma wayar da kan al’umomi kan muhimmancin tsafta da kwana cikin gidan sange mai magani, da kuma zuwa asibitoci da zaran aji ba’a da lafiya.

Daga karshe a cewar wannan sanarwa ta hukumomin kiwon lafiya na ofishin DRSP reshen Zinder, gwamnatin Nijar ta tanadi magunguna da sauran kayayyaki domin hana cutar zama wata annoba. (Mamane Ada)