Shugaban majalisar dokokin Kenya zai ziyarci kasar Sin
2024-09-19 14:42:25 CMG Hausa
Bisa goron gayyatar da shugaban zaunannen kwamitin majalisar wakilan jama’ar kasar Sin Zhao Leji ya mika masa, shugaban majalisar dokokin kasar Kenya Moses Masika Wetangula, zai jagoranci tawagar jami’an kasarsa domin gudanar da ziyarar aiki a kasar Sin daga ranar 21 zuwa 26 ga watan nan. (Bilkisu Xin)