logo

HAUSA

Sojojin Nijar sun sanar da hallaka sama da ‘yan ta’adda 100

2024-09-19 10:58:08 CMG Hausa

Rundunar sojojin janhuriyar Nijar ta ce ta yi nasarar hallaka sama da ‘yan ta’adda 100, tare da lalata wasu tarin kayayyakin yakin da suke amfani da su, sakamakon hare hare ta kasa da sama da sojojin suka kaddamar a yankin Niaktire, dake kusa da garin Makalondi na jihar Tillabery.

Rahotanni daga rundunar na cewa, dakarun rundunar ta FDS dake girke a  Niaktire, sun fuskanci farmaki daga daruruwan ‘yan ta’adda da yammacin ranar Lahadi, kuma nan take sojojin suka mayar da martani, inda bayan dauki ba dadi na tsawon lokaci, sojojin gwamnatin suka yi nasara kan bata garin, inda suka hallaka da daman su.

Rundunar ta kara da cewa, sakamakon aukuwar harin, an gaggauta aikewa da karin rukunonin sojojin musamman daga Torodi da kuma Makalondi zuwa wurin. A lokaci guda kuma, an kaddamar da hare hare ta sama domin kakkabe gyauron ‘yan ta’addan daga maboyarsu. (Saminu Alhassan)