logo

HAUSA

Mene ne dalilin da ya sa kamfanonin waje su zuba jari ga kasar Sin?

2024-09-18 21:18:15 CMG Hausa

An gudanar da bikin baje kolin zuba jari da cinikayya na kasa da kasa na kasar Sin karo na 24 (CIFIT) a birnin Xiamen na lardin Fujian dake kasar tun daga ranar 8 zuwa 11 ga wannan wata, kuma an kebe wani bangare na musamman na zuba jari ga kasar Sin karo na farko, da mai da hankali ga sabon karfin samar da hajoji da hidimomi masu karko, kuma ‘yan kasuwa kimanin dubu 80 daga kasashe da yankuna 120 sun halarci bikin. Bisa kididdigar da aka yi, an cimma yarjejeniyoyin hadin gwiwa 688 a yayin bikin, yawan jarin da aka shirya zubawa ya kai Yuan biliyan 488.92.

Bikin shi ne biki na farko da Sin ta gudanar game da batun zuba jari bayan da aka gudanar da cikakken zama na 3 na kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20, wanda ya kasance muhimmin dandalin fahimtar Sin da neman dama a Sin ga kamfanonin kasashen waje. Wakilan kamfanonin kasa da kasa sun bayyana cewa, ya kamata a rungumi damar kasuwar kasar Sin, an yawaita ambaton kalmomin “zuba jari ga kasar Sin” a yayin bikin.

Kasuwar kasar Sin ta kiyaye samar da dama ga duniya. An kiyaye kyautata tsarin kashe kudi, da sa kaimi ga samar da kayayyaki da hidimomi masu inganci. Haka zalika kuma kasar Sin tana da kwarewa wajen samar da kayayyaki, hakan ya ba da tabbaci ga kamfanonin kasashen waje da su zuba jari da gudanar da ayyukansu. Kana kirkire-kirkire ya zama muhimmin karfi wajen sa kaimi ga bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin, saboda karin kamfanonin kasashen waje sun maida kasar Sin a matsayin wurin yin kirkire-kirkire. A yayin bikin a wannan karo, an gabatar da rahoton zuba jarin Sin da kasar ta zuba a kasashen waje na shekarar 2024, an ce, kasar Sin ta kasance kasa ta biyu mafi jawo jarin waje a duniya a shekarar 2023, Sin ta ci gaba da kasancewa kasa mafi jawo jarin kasa da kasa a duniya. (Zainab Zhang)