logo

HAUSA

Sanar da kwaskwarimar karin haraji kan hajojin kasar Sin dake shiga Amurka zai haifarwa Amurkar matsala

2024-09-16 16:57:41 CMG Hausa

Masanan sana’o’i da tattalin arziki na kasar Amurka, sun nuna damuwa sosai da matakin ofishin wakilcin hada-hadar cinikayya na kasar, na yin kwaskwarimar karin haraji kan hajojin kasar Sin dake shiga kasar.

Ko da yake an samu ra’ayoyin kin amincewa da karin harajin da neman fadada fannonin soke harajin kwastam, gwamnatin Amurka ta yi biris da su, inda ta nace wajen daukar matakanta. Irin wannan ra’ayi da bangare daya ke dauka da ba da kariya ga cinikayya, ya saba da alkawarin Amurka na cewa ba za ta hana bunkasuwar Sin ko yanke hulda da Sin ba. Kana ra’ayin ya sabawa daidaiton da shugabannin kasashen biyu suka cimma, da shaida cewa Amurka ba ta cika alkawarinta ba.

Manazarta na ganin cewa, Amurka tana amfani da harajin kwastam wajen cimma yunkurinta a siyasa. Yayin da ake gab da lokacin zaben shugaban Amurka, takara na kara zafi tsakanin jam’iyyun biyu na kasar, kuma wadda ta fi nuna karfi ga kasar Sin, ita ce wadda za ta samu fifiko a siyasa.

Lamura da dama sun shaida cewa, kwaskwarimar karin haraji kan hajojin kasar Sin dake shiga Amurka wato kudurin doka mai lamba 301 ba za ta samu goyon baya ba, yunkurin Amurka kan hana bunkasuwar kamfanonin Sin da sana’o’in da abin ya shafa ta hanyar buga karin harajin kwastam bai samu nasara ba. Ya kamata Amurka ta gyara kuskurenta, ta soke dukkan karin harajin da aka bugawa kasar Sin. Kasar Sin a nata bangare, za ta dauki matakai don tabbatar da moriyar kamfanoninta. Kuma babu wanda zai iya hana farfadowa da bunkasuwar kasar Sin. (Zainab Zhang)