logo

HAUSA

Gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara aikin gyaran makarantun sakandaren kasar da suke a lalace

2024-04-26 09:34:27 CMG Hausa

Gwamnatin  tarayyar Najeriya ta ce nan ba da jimawa ba za ta fara aikin gyaran makarantun sakandaren kasar da suke a lalace a dukkan jahohi 36 ciki har da Abuja.

Babban sakataren hukumar lura da ilimin sakandare na kasa Dr. Iyela Ajayi ne ya tabbatar da hakan  lokacin da ya kai ziyara ma`aikatar ilimi ta jihar Nasarawa dake arewa masu tsakiyar Najeriya, yace za a gudanar da aikin ne kashi-kashi.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

Babban sakatare a ma`aikatar ilimi ta jihar Nasarawa Muhammad Sani Bala ne ya tarbi tawagar hukumar.

Da yake jawabi Dr. Iyela Ajayi ya ce gwamnati ta lura sosai da yawa daga cikin makarantun sakadaren kasar suna cikin yanayi mara kyau na rashin ingantattun dakunan daukar darussa da na gwaje gwajen kimiyya da kuma ban dakuna.

Ya ce ya ziyarci jihar Nasarawa ne domin tattauna bangarorin da za su samu hadin gwiwa tsakanin jihar da gwamnatin tarayya wajen ganin an samu nasarar shirin aikin kwaskwarima ga makarantun.

“Manyan makarantun sakandare a kasar nan guda 50 ne za su fara amfana da shirin a kashin farko, kuma ina tabbatar maka cewa jihar Nasarawa tana daya daga cikin wadanda za su fara amfana, a don haka ne muka kawo wannan ziyara domin neman hadin kan gwamnatin jihar ga  `yan kwangilar da za su gudanar da aikin”

A jawabinsa, babban sakatare a ma`aikatar ilimi ta jihar Nasarawa Muhammad Sani Bala yayi alkawarin samun cikakken hadin kai da goyon bayan gwamnatin jihar.(Garba Abdullahi Bagwai)