logo

HAUSA

An bude dandalin Zhongguancun a nan birnin Beijing

2024-04-25 15:36:40 CMG Hausa

A yau Alhamis ne aka fara taron dandalin Zhongguancun na shekarar 2024 a nan birnin Beijing, inda za a mai da hankali kan manyan fannonin fasahohi, daga kirkirarriyar basira wato AI, zuwa kimiyyar rayuwa da sabbin kayayyaki a yayin zaman na kwanaki biyar da za a gudanar har zuwa ranar Litinin mai zuwa.

Taron na bana mai taken “Kirkire-kirkire don samar da ingatacciyar duniya” ya kunshi manyan sassa biyar da suka hada da tarurruka da cinikayyar fasaha.

Gasannin da ake yi a fagage masu inganci sun jawo sama da ayyuka 3,100 daga kasashe da yankuna 75, yayin da taron cinikayyar fasaha ya jawo ayyuka sama da 6,000 daga kasashe da yankuna sama da 40. (Yahaya)