logo

HAUSA

Kasar Sin Na Fatan Amurka Za Ta Girmama Ka’idojin Takara Bisa Adalci

2024-04-25 20:10:09 CMG Hausa

Ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ta ce, nan ba da jimawa ba, za ta yi karin haske game da ziyarar sakataren harkokin wajen Amurka a kasar Sin.

Kakakin ma’aikatar Wang Wenbin ne ya bayyana haka a yau, yayin taron manema labarai da aka saba yi a kullum, bayan an nemi jin ta bakinsa game da tsokacin da sakataren harkokin wajen Amurka Anthony Blinken ya yi yayin ziyararsa a Shanghai. Wang Wenbin ya bayyana cewa, sun riga sun gabatar da makasudin ziyarar jami’in na Amurka, kwanaki biyun da suka gabata, tare kuma da bayyana matsayin kasar Sin kan batun.

Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin ta kasance mai aiwatar da hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya bisa ka’idojin kasuwa, haka kuma ta kasance mai nacewa ga tsarin cinikayya tsakanin bangarori da dama da kuma aiwatar da ka’idojin hukumar kula da cinikayya ta duniya (WTO) yadda ya kamata. A cewarsa, ana fata bangaren Amurka zai martaba ka’idojin takara bisa adalci da biyayya ga ka’idojin WTO da hada hannu da kasar Sin wajen samar da kyakkyawan yanayin raya dangantakar tattalin arziki da cinikayya dake tsakaninsu cikin aminci. (Fa’iza Mustapha)