logo

HAUSA

Xi ya yi kira da a gina manyan jami’o’in kiwon lafiya na soji

2024-04-25 10:56:43 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi kira da a gina manyan jami’o’in kiwon lafiya na soja a matsayin kolin duniya, yana mai jaddada cewa, kamata ya yi su ba da hidima a fagen daga da runduna, da kuma la’akari da gaba.

Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin koli na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, kana shugaban kwamitin koli na soja, ya bayyana hakan ne yayin da ya kai rangadi a jami'ar kiwon lafiya ta sojoji a ranar Talata. (Yahaya)