logo

HAUSA

Ana fatan baje koli na Canton Fair zai samu sabon ci gaba a sabon zamani

2024-04-24 07:38:18 CMG Hausa

An bude baje kolin hajojin da ake shigowa, gami da wadanda ake fitarwa zuwa ketare na kasar Sin wato “Canton Fair” a tsakiyar watan nan na Afirilu, bikin da ya zamo karo na 135. An fara gudanar da shi ne tun daga lokacin bazarar shekara ta 1957, kuma ake ci gaba da yin sa sau biyu a kowace shekara a birnin Guangzhou, na larding Guangdong, wato a lokutan bazara da na kaka.

Tarihin baje kolin tun bayan fara gudanar da shi, ya shaida yadda kamfanonin kasa da kasa ke more damammakin ci gaban kasar Sin, da cimma burin samun moriya tare, wanda kuma ke bayyana yadda kasar ke kokarin fadada bude kofarta ga kasashen waje, da shiga cikin kasuwannin duniya.

Mashirya baje kolin sun sha alwashin amfani da shi wajen kara fadadawa, da bude kofofin kasar Sin ga sauran kasashen duniya, da saukaka hada hadar kasuwanci da zuba jari, da ci gaba da samar da tabbaci ga harkokin cinikayya da tattalin arzikin duniya bisa ci gaban Sin, tare kuma da samar da damammaki masu yawa ga kamfanonin kasa da kasa.

Mahalarta bajen na wannan karo dake gudana tsakanin ranaikun 15 ga watan nan zuwa 5 ga watan Mayu, na ta bayyana imaninsu ga makomar tattalin arzikin kasar Sin, tare da fatan ci gaba da fadada kasuwanci a kasar Sin, da bayar da gudummawa ga gudanar da kasuwanci cikin ‘yanci, da tabbatar da samar da kayayyaki ga duniya yadda ya kamata, ta hanyar halartar Canton Fair.

A wannan karo, ababen hawa masu amfani da lantarki, da batiran makamashin hasken rana, da batiran “lithium-ion”, bangarori ne uku da Sin ke fadada cin gajiyar fasahohin su, musamman kasancewarsu bangarorin raya makamashi maras gurbata muhalli. (Sanusi Chen, Saminu Alhassan, Faeza Mustapha)