logo

HAUSA

Sin na shirin harba kumbon Shenzhou-18 mai dauke da ‘yan sama jannati

2024-04-24 14:34:34 CMG Hausa

Yanzu haka shirye shirye sun kammala, na harba kumbon Shenzhou-18 mai dauke da ‘yan sama jannati, inda ake sa ran harba kumbon a daren gobe Alhamis, da karfe 9 saura minti daya agogon birnin Beijing.

Yayin taron ganawa da manema labarai da ya gudana a Larabar nan, mataimakin daraktan hukumar lura da binciken sararin samaniya ta Sin ko CMSA Lin Xiqiang, ya ce za a harba kumbon Shenzhou-18 ne daga tashar Jiuquan dake arewa maso yammacin kasar Sin. Kuma zai tashi tare da ‘yan sama jannati uku, Ye Guangfu, da Li Cong da Li Guangsu, karkashin jagorancin Ye.

Lin ya kara da cewa, Shenzhou-18 zai kasance kumbo na 32 da kasar Sin za ta harba dauke da ‘yan sama jannati, karkashin shirin ta na binciken samaniya, kana karo na 3 tun bayan kaddamar da matakin aiwatarwa, da bunkasa shirin tashar sararin samaniya kasar.

Jami’in ya ce ‘yan sama jannatin za su kasance cikin falakin kumbon har tsawon kusan watanni 6, kana za su sauko a wurin saukar kumbuna na Dongfeng dake yankin Mongolia ta gida a karshen watan Oktoban bana.

Lin Xiqiang, ya kuma ce tsarin saukar kumbuna na kasar Sin yana gudana yadda ya kamata, kasancewar kasar na gudanar da karin bincike da bunkasa ayyukan na’urorin fannin kamar yadda aka tsara. Ya kuma ce nan da dan lokaci kadan, za a kammala zaben rukuni na 4 na ‘yan sama jannatin kasar Sin.  (Saminu Alhassan)