logo

HAUSA

Kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar Sin ya fara taronsa karo na 9

2024-04-23 13:10:52 CMG Hausa

Kwamitin dindindin na majalisar wakilan jama’ar kasar Sin ta 14, ya kaddamar da taro karo na 9 a yau Talata, domin nazarin kudurorin doka da sake bitar wasu dokoki.

Ajandar taron ta hada da sake nazarin dokar shaidar karatun digiri da kudurin dokar da ta shafi haraji da kudurin sake bitar dokar ilimin tsaron kasa da kudurorin gyaran dokokin hada-hadar kudi da na kiddidiga, da kudurin dokar makamashi, da kudurin dokar makamashin nukiliya da kuma kudurin bitar dokar yaki da halatta kudin haram da sauransu. (Fa’iza Mustapha)