logo

HAUSA

Xi: Walwalar jama’a muhimmin batu ne ga aikin zamanantar da kasar Sin

2024-04-23 15:48:32 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya ce walwalar jama’a abu ne mai matukar muhimmanci ga zamanantar da kasar Sin. Shugaban wanda kuma shi ne sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS ya bayyana haka ne yayin rangadin da ya yi a birnin Chongqing dake kudu maso yammacin kasar a jiya, inda ya ce manufar JKS ita ce, tabbatar da jama’a suna rayuwa cikin farin ciki.

Xi Jinping ya kuma jaddada cewa, ya zama wajibi a fayyace iko da nauyin da ya rataya a wuyan wadanda suke aiki a matakin farko, domin rage masu nauyi.

Shugaban ya bayyana haka ne lokacin da ya ziyarci wata unguwa dake yankin Jiulongpo, wadda aka yi wa gyaran fuska kuma take cikin yanayi mai kyau.

Haka kuma, ya ziyarci cibiyar kula da harkokin unguwar, yana mai tambayar ma’aikata ayyukan da suke gudanarwa da albashinsu da yawan ayyukansu, domin fahimtar yadda yunkurin ragewa ma’aikata yawan ayyuka a matakin unguwanni ke yin tasiri a shekarun baya-bayan nan. (Fa’iza Mustapha)