logo

HAUSA

Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai ziyarci kasar Sin

2024-04-22 16:05:50 CMG Hausa

Kakakin ma’aikatar harkokin wajen Sin Wang Wenbin ya sanar a yau Litinin cewa, bisa gayyatar da mamban hukumar siyasa ta kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, kuma ministan harkokin wajen kasar Wang Yi ya yi masa, sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken zai kawo ziyara kasar Sin daga ranar 24 zuwa ranar 26 ga wannan wata. (Safiyah Ma)