logo

HAUSA

Kasar Sin Ta Wallafa Jerin Taswirar Labarin Kasa Ta Duniyar Wata, Irinsu Na Farko

2024-04-21 16:37:11 CMG Hausa

Kasar Sin ta fitar da jerin taswirar labarin kasa ta duniyar wata, mai zanen tazarar taswira maki 1 kan duk miliyan 2 da rabi, wanda shi ne irinsa na farko a duniya mai dauke da cikakkun hotunan labarin kasa ta duniyar wata, wanda kuma ya gabatar da muhimman bayanan duniyar domin gudanar da bincike a nan gaba.

A cewar cibiyar nazarin alakar labarin kasa da sinadarai wato Geochemistry, ta kwalejin nazarin kimiyya ta kasar Sin, cikin jerin taswirar da aka wallafa cikin harsunan Sinanci da Ingilishi, akwai taswirar duniyar wata da kuma ta shimfida da siffarta.

A cewar Ouyang Ziyuan, masanin kimiyyar duniyar wata na cibiyar nazarin kimiyya ta kasar Sin, jerin taswirar labarin kasa ta duniyar watan na da matukar muhimmanci wajen nazarin yanayin duniyar wata, da zabo wuraren da za a gina tashar bincike a nan gaba, da kuma cin gajiyar albarkatun watan. Haka kuma zai taimaka wajen kara fahimtar duniyar dan Adam da sauran duniyoyin dake kewayen rana, kamar duniyar Mars. (Fa’iza Mustapha)