logo

HAUSA

Kusan 90% na masu amsa tambayoyin duniya sun yaba da gudummawar da Sin ke bayarwa ga bunkasuwar duniya irin na kiyaye muhalli, a cewar Binciken Jin Ra’ayin Jama’a na CGTN

2024-04-21 00:27:23 CMG Hausa

A daidai lokacin da motoci masu amfani da sabbin makamashi da batirin lithium, da kayayyakin samar da wutar lantarki ta hasken rana na kasar Sin, suke ta samun karbuwa a kasuwannin duniya, wasu kasashen yammacin duniya sun zargi kasar Sin da cewa, wai ta “wuce gona da iri" wajen samar da hajoji masu amfani da sabbin makamashi.

Sai dai wani binciken jin ra'ayin al'ummar kasashen duniya da kafar CGTN karkashin babban rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin, wato CMG a takaice, ya gudanar a baya-bayan nan, ya nuna cewa, kashi 88.62% na masu amsa tambayoyin duniya sun tabbatar da gudummawar da masana’antu masu nasaba da sabbin makamashi na kasar Sin ke bayarwa ga tattalin arzikin duniya da ma bunkasuwar duniya ba tare da gurbata muhalli ba, baya ga kaso 77.41% na masu amsa bambayoyin sun yi imanin cewa, hada kariyar ciniki tare da masana’antu masu nasaba da sabbin makamashi zai raunana kokarin kasashe daban daban na yin aiki tare don magance sauyin yanayin duniya.

An fitar da wannan binciken ne a dandalin CGTN na Turanci, Sipaniya, Larabci, Faransanci, da Rashanci, inda jimillar masu amfani da yanar gizo 5470 daga ketare suka shiga binciken tare da bayyana ra'ayoyinsu cikin sa'o'i 24. (Mai fassara: Bilkisu Xin)