logo

HAUSA

Bangaren kera jiragen ruwa na kasar Sin yana ci gaba da bunkasa

2023-11-18 11:23:44 CMG Hausa

              

Bayanai na nuna cewa, a cikin watanni 10 na farkon shekarar 2023, kasar Sin ta ci gaba da rike matsayinta na zama jagora, a kasuwar kera jiragen ruwa ta duniya, tare da samun ci gaba mai karfi a bangaren jiragen ruwan da ake fitarwa da ma sabbi da aka yi oda.

Alkaluman da kungiyar masana'antun kera jiragen ruwa ta kasar ta fitar na nuna cewa, yawan jiragen ruwa da kasar ta kera, ya karu da kashi 12 cikin 100 a duk shekara zuwa tan miliyan 34.56 (dwt) a tsakanin watan Janairu zuwa Oktoba, wanda ya kai kashi 49.7 na jimillar jiragen ruwan da aka samar a duniya.

Sabbin jiragen ruwan da aka yi oda, sun karu da kashi 63.3 kan na shekarar bara, zuwa tan miliyan 61.06, wanda ya kai kashi 67 cikin 100 na jimillar adadin da aka yi oda a duniya a cikin wannan wa’adi.

A cikin watanni 10 na farkon bana, masu kera jiragen ruwa na kasar Sin, sun fitar da jiragen ruwa zuwa ketare da darajarsu ta kai dalar Amurka biliyan 21.14, wanda ya karu da kashi 21 cikin 100 idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata. (Ibrahim)