logo

HAUSA

Kasuwar kasar Sin mai bude kofa za ta kara samar da dama ga bunkasuwar kamfanonin kasa da kasa

2023-03-05 10:41:02 CMG Hausa

Bisa rahoton aikin gwamnatin kasar Sin da aka gabatar a yau, an ba da shawara kan aikin gwamnatin kasar na shekarar 2023, inda aka bayyana cewa, ya kamata a kara jawowa tare da amfani da jarin waje, rahoton yana mai cewa, kasuwar kasar Sin mai bude kofa, za ta kara samar da dama ga bunkasuwar kamfanonin kasa da kasa dake kasar.

Rahoton aikin gwamnatin ya bayyana cewa, ya kamata a kara ba da iznin shiga kasuwar kasar, da kara bude kofa ga kasashen waje a fannin samar da hidima. Kana a kare hakkin kamfanoni masu jarin waje, da sa kaimi ga daddale yarjejeniyoyin tattalin arziki da cinikayya masu inganci kamar yarjejeniyar CPTPP ta kasashen yankin tekun Pasifik da ta shafi dukkan bangarori, da kuma fadada bude kofa ga kasashen waje bisa tsarin kasar.

Kana rahoton ya yi nuni da cewa, ya kamata a ci gaba da amfani da harkokin shige da fice wajen goyon bayan bunkasuwar tattalin arzikin kasar Sin. Haka kuma za a tabbatar da samar da hidima ga kamfanoni masu jarin waje don kara musu kwarin gwiwar fara aiwatar da manyan ayyuka a kasar. (Zainab)