logo

HAUSA

An yi taron manema labarai kan zaman farko na kwamitin majalisar CPPCC karo na 14

2023-03-03 21:40:16 CMG Hausa

An yi taron manema labarai kan zaman farko na kwamitin majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasar kasar Sin karo na 14 wato CPPCC a takaice da yammacin yau Jumma’a a babban dakin taron jama’a dake birnin Beijing na kasar Sin.

Ga rahoton da Murtala Zhang ya hada.

A wajen taron manema labarai na yau, kakakin taron majalisar bada shawarwari kan harkokin siyasa na kasar Sin, Guo Weimin ya yi karin haske kan zaman farko na kwamitin majalisar CPPCC karo na 14, wanda za’a fara gudanarwa daga gobe Asabar, har zuwa ranar 11 ga watan Maris din nan da muke ciki.

Guo ya ce, kwamitin majalisar CPPCC karo na 14 yana kunshe da membobi 2169, wadanda suka shafi bangarori 34.

A yayin zaman taron na tsawon kwanaki 7 da rabi, membobin majalisar CPPCC za su gudanar da shawarwari kan harkokin siyasa, da sa ido bisa tafarkin demokuradiyya, da shiga harkokin siyasa, wadanda za su bayar da shawarwari a fannonin da suka shafi siyasa, tattalin arziki, zamantakewar al’umma, al’adu, muhallin halittu, ilimi da sauransu. (Murtala Zhang)