logo

HAUSA

An gudanar da baje kolin hotunan tashar samaniya ta Sin

2023-01-24 15:21:46 CMG Hausa

An gudanar da baje kolin musamman, na hotunan tashar sararin samaniya ta Sin da ake kira Tiangong, wadda ke kan falaki mai nisan kilomita kusan 400 daga doron duniya, a matsayin wata kyautar murnar bikin bazara na gargajiyar kasar Sin.

‘Yan sama jannatin kumbon Shenzhou-15, wato Fei Junlong, da Deng Qingming da Zhang Lu, sun gabatar da hotuna 21, na tashar samaniyar ta Sin wadanda aka dauka daga doron duniya, hotunan da suka fayyace kayatattun sassa na tashar daga bangarori daban daban.

Hotunan dai bangare ne na jimillar hotunan da aka tattara karkashin shirin "Global Lens on Tiangong", wanda aka fara hadawa a watan Nuwamban shekarar 2021. Shirin ya ja hankalin sassa da dama na kwararrun masu daukar hotuna, da masu sha’awar harkokin sama jannati, da masana kimiyyar samaniya, da matasa, inda karkashin sa aka tara hotuna da yawan su ya kai sama da 10,000, masu dauke da sassan tashar samaniya ta Sin.

An dai harba kumbon Shenzhou-15 ne a matsayin matakin karshe na ginin tashar sararin samaniya ta Sin, tare da shiga matakin farko na aiki da ita, da ci gaba da bunkasa ta. (Saminu Alhassan)