logo

HAUSA

AFDB: Karuwar tattalin arzikin gabashin Afirka za ta kai kaso 4.7 cikin 100 a shekarar badi

2022-11-29 15:31:37 CMG Hausa

Wani sabon hasashen tattalin arzikin gabashin Afirka na shekarar 2022 da bankin raya kasashen nahiyar Afirka ya fitar a baya-bayan nan, ya nuna cewa, karuwar tattalin arzikin yankin gabashin Afirkar, za ta kai kaso 4.7 bisa 100 a shekarar 2023.

Rahotanni na cewa, sakamakon karuwar farashin makamashi da kayayyakin abinci, da tafiyar hawainiya kan tsarin samar da kayayyaki a duniya, da tasirin bala’u, hauhawar farashin kayayyaki ya ci gaba da karuwa, kana karuwar tattalin arziki a yankin gabashin Afirka, za ta ragu zuwa kashi 4.0 cikin 100. A shekarar 2023, tattalin arzikin nahiyar, zai farfado zuwa kashi 4.7 cikin100, yankin da ake ganin zai sake kasancewa a kan gaba wajen ci gaban tattalin arziki a nahiyar Afirka. (Ibrahim)