logo

HAUSA

Kasar Sin ta yi kira da a inganta tsarin tafiyar da fasahar AI

2022-11-17 10:38:24 CMG Hausa

A jiya ne kasar Sin ta gabatarwa taron manyan jami’an sassan da suka sanya hannu kan yarjejeniyar hana amfani da wasu makamai na al’ada da aka gudanar a birnin Geneva, takardar da ke bayyana matsayinta game da bukatar karfafa tsarin dokar tafiyar da fasahar kwaikwayon tunanin dan-Adam (AI).

Jakadan kasar Sin mai kula da harkokin kwance damara Li Song, ya fadawa mahalarta taron cewa, a matsayinta na babbar hanyar samar da fasahohi da za ta iya kawo tsaiko ga al’umma, a gabar da kuma take samar da fa’idoji masu tarin yawa da daukacin bil-Adama, fasahar AI ta kuma haifar da yanayi na rashin tabbas da ka iya bijiro da kalubale da dama a duniya, baya ga matsalolin da suka shafi doka.

Takardar matsayin da kasar Sin ta gabatar a jiya, ta nuna cewa, ya kamata gwamnatoci su rika dora muhammanci kan doka, da kafawa da kuma inganta dokoki, da ka’idoji da matakan da za a rika bi wajen tabbatar da ka’idojin da suka shafi tafiyar da fasahar ta AI, da fayyace nauyi da ikon da sassan dake da alaka da fasahar ke da shi, da mutuntawa da kare ’yanci da muradun dukkan kungiyoyi, da amsa matsalolin da suka shafi doka a cikin gida da waje a kan lokaci. (Ibrahim Yaya)