logo

HAUSA

CMG Ya Rattaba Hannu Kan Takardar Bayanin Hadin Gwiwa Da Gidan Rediyon Indonesia

2022-11-16 20:30:23 CMG Hausa

Yayin da shugaban kasar Sin ke ziyara a tsibirin Bali na kasar Indonesia domin halartar taron koli na 17 na kungiyar G20, shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG Shen Haixiong, da takwaransa na gidan rediyon Indonesia I Hendrasmo, sun rattaba hannu kan takardar bayanin hadin gwiwa tsakanin kafafen watsa labaran biyu.

Takardar bayanin daya ne daga cikin nasarorin hadin gwiwa a bangaren watsa labarai da kasashen biyu suka samu, karkashin jagorancin shugabannin kasashen na Sin da Indonesia. (Fa’iza Mustapha)