logo

HAUSA

Matakan sojan da Amurka ke dauka a kasashen waje sun shaida babakeren da take yi

2022-09-20 21:05:31 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana a yau talata cewa, kasar Sin ta lura da alkaluman da suka shafi matakan sojan da kasar Amurka ke dauka a kasashen waje. Duk da cewa Amurka ta yi ikirarin cewa, tana mutuntawa, gami da kiyaye dokokin kasa da kasa bisa tushen ka’ida, amma alkaluman sun shaida son nuna fin karfi da babakere irin nata.

Rahotanni sun ce, wani dan jarida mai zaman kansa mai suna Benjamin Norton, ya ruwaito alkaluman da sashin binciken hidimomi na majalisar dokokin Amurka ya fitar, wadanda suka nuna daga shekara ta 1798 zuwa ta 2022, gaba daya Amurka ta aiwatar da matakan soja har sau 469 a kasashen ketare, kana, daga kawo karshen yakin cacar baka zuwa yanzu, Amurka ta dauki matakan soja har sau 251 a cikin shekaru sama da 30.

Rahotannin sun kuma ce, Amurka ta dauki matakan soja a kasashe masu tarin yawa, ciki har da kusan dukkanin kasashen dake Latin Amurka, da yawancin kasashen Afirka. (Murtala Zhang)