logo

HAUSA

Xi ya gana da takwaransa na Uzbekistan

2022-09-15 19:59:57 CMG Hausa

Alhamin din nan ne agogon kasar, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya tattauna da takwaransa na kasar Uzbekistan Shavkat Mirziyoyev a birnin Samarkand. Yayin ganawar, shugabannin kasashen biyu sun sanar da cewa, bisa la'akari da yadda ake raya dangantakar dake tsakanin kasashen biyu na dogon lokaci, da kyautata zaman rayuwar al’ummomin kasashen biyu a nan gaba, bangarorin biyu za su fadada alakar moriyar juna, da karfafa zumunci da hadin gwiwa.

Haka kuma, shugaba Xi ya karbi lambar yabo ta "Supreme Friendship" da Mirziyoyev ya ba shi. (Ibrahim)