logo

HAUSA

An kaddamar da cikakken zama karo na 77 na babban taron MDD

2022-09-14 13:50:17 CMG Hausa

 

An kaddamar da cikakken zama karo na 77 na babban taron MDD a Talata a birnin New York, inda hedikwatar MDD take. Shi ne taron MDD na farko da za a gudanar ido da ido, tun bayan barkewar cutar COVID-19.

Babban sakataren MDD António Guterres, ya ba da jawabi a yayin bude taro, inda ya ce, a yanzu duniya tana cikin hadari, duba da yadda ake fuskantar kalubaloli iri iri, a fannin inganta zaman lafiya, da ikon bil’adam da kuma ci gaba mai dorewa. Ya ce rikice-rikice, da sauyin yanayi, da talauci, da rashin daidaito, da yunwa, da rashin amincewar juna, da sauran barazana da kalubaloli suna nuni ga bukatar dukkanin sassa su hada kai da juna. (Safiyah Ma)