logo

HAUSA

Kasar Sin ta sake bayyana matsayinta kan rahoton ofishin OHCHR dangane da jihar Xinjiang

2022-09-02 20:50:25 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya sake bayyana matsayin kasarsa, kan rahoton da ofishin babban kwamishinan Majalisar Dinkin Duniya mai lura da hakkokin bil’adama, ko kuma OHCHR a takaice ya fitar, wanda ya shafi jihar Xinjiang ta kasar Sin, tare da kira ga kasashe membobin MDD da su dora laifi kan OHCHR.

Zhao Lijian ya ce, rahoton cike yake da karairayi, wanda kasar Amurka tare da sauran wasu kasashen yammacin duniya suka kirkiro don cimma muradunsu na siyasa, kana, ya sake shaida cewa, ofishin OHCHR ya riga ya zama mai hada baki da Amurka, da sauran wasu kasashen yamma wajen lalata kasashe masu tasowa.

Zhao ya kara da cewa, kwanan nan ne kasashe sama da 60, suka gabatar da sako zuwa ga ofishin OHCHR, inda suka jaddada cewa, batun jihar Xinjiang, batun cikin gidan kasar Sin ne zalla, don haka sun nuna matukar damuwa kan irin wannan rahoton da ofishin ya rubuta ba tare da samun izini daga kasar Sin ba.

Haka kuma kungiyoyin da ba na gwamnati ba kusan dubu 1 na gida da na waje, sun rubuta wasika ga OHCHR, inda suka nuna adawarsu kan abun da ofishin ya yi, wato gabatar da wani rahoto game da Xinjiang wanda ya jirkita gaskiya.

Zhao ya kuma nuna cewa, a matsayinsa na wani sashi na sakatariyar MDD, ya zama dole OHCHR ya girmama ka’idojin tsarin mulkin majalisar, kana, bai kamata ya yi shisshigi cikin harkokin cikin gidan kasashe membobinta ba. Amma rahoton da OHCHR ya fitar game da Xinjiang, wanda ke karkashin makircin Amurka da sauran wasu kasashen yammacin duniya, ya saba wa hakan. (Murtala Zhang)