logo

HAUSA

Wakilin Sin a MDD ya bukaci da a gaggauta dage takunkuman da aka kakaba wa kasar Syria

2022-07-22 10:56:35 CMG Hausa

 

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Dai Bing, ya bukaci kasashen da abin ya shafa, da su gaggauta dage takunkuman kashin kai da suka kakaba wa kasar Syria, kana ya yi kira ga kwamitin sulhu na MDD, da ya samar da wani shiri na zahiri da zai kai cimma wannan buri.

Dai Bing, ya shaidawa taron muhawara na babban zauren MDD cewa, “a koda yaushe muna goyon bayan MDD da kasashen duniya, wajen kai agajin jin kai ga 'yan kasar Syria, bisa ka'idojin da suka shafi bil-Adama, ba tare da nuna son kai ba."

Ya ce, takunkuman kashin kai da aka sanyawa kasar, sun haifar da mummunan tasiri ga farfadowar tattalin arziki da ci gaban zamantakewa, ta hanyar kawo cikas ga ayyukan hukumomin jin kai na kasa da kasa dake kasar.

Wakilin na kasar Sin ya kara da cewa, irin wadannan matakai, sun kasance babban cikas ga warware matsalar jin kai na kasar. Don haka, tilas ne a gaggauta cire su gaba daya. Kuma wajibi ne kwamitin sulhu, ya samar da shiri na zahiri kan wannan batu.(Ibrahim)