logo

HAUSA

Rahoto: Iran ta zargi Amurka da kasancewa mafi keta hakkokin bil adama

2022-07-07 14:10:19 CMG Hausa

Wani rahoton bincike game da yanayin kare hakkin bil adama, da yadda ake aiwatar da matakan sa a Amurka, wanda gwamnatin kasar Iran ta fitar, ya zargi Amurka da kasancewa kasa ta daya, a fannin keta kakkokin bil adama.

Yayin makon nazarin kare hakkin bil adama na Amurka, wanda mahukuntan Iran din suka gudanar, tsakanin ranakun 27 ga watan Yuni zuwa 3 ga watan nan na Yuli, rahoton shekara shekara da ma’aikatar harkokin wajen Iran din ke fitarwa, ya ce kasar Iran na cikin jerin kasashen da Amurka ke ketawa hakkin bil adama. Kaza lika a yanzu haka ma, takunkuman da Amurkan ta kakabawa Iran sun zamo wani makami na keta hakkokin Iraniyawa.

Rahoton ya ce, takunkuman da Amurka ke kakabawa Iran muggan ayyukan ta’addanci ne a fannin tattalin arziki, wadanda ke yin mummunan tasiri ga harkokin sarrafa kayayyaki, da samar da guraben ayyukan yi, da kudaden shigar kasar, duba da yadda suke raunata karfin tattalin arziki, da takaita kudaden shiga, wanda hakan ke rage ingancin rayuwar Iraniyawa.

Har ila yau, rahoton ya zargi Amurka da shake makoshin Iran, ta hanyar hana kasar fitar da danyen man ta zuwa kasuwannin duniya. Wanda dalilin hakan ya sa kudaden shigar kasar ya yi matukar raguwa, lamarin da ya kuma ya haifar da gazawar gwamnati, na kiyaye da kyautata manyan ababen more rayuwa a Iran.

Masharhanta na cewa, katse damar Iran ta shiga harkokin hada hadar kudade na kasa da kasa, da hana ta damar cinikayya bisa tsarin zamani da sauran sassan duniya, ya yi matukar haifar wa kasar koma baya a wadannan fannoni, ya kuma haifar da cikas ga burin kasar na bunkasawa, da kyautata masana’antun ta.  (Saminu)